Mutum ɗaya ya rasa ransa, yayin da wasu ma’aikata bakwai suka jikkata sakamakon rushewar wani sashe na sabon ginin Majalisar Dokokin Jihar Gombe da ake ginawa.
Babban Sakataren Ma’aikatar Ayyuka, Gidaje da Sufuri ta Jihar Gombe, Danladi Adamu, ne ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a ranar Juma’a.
Adamu ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, yana mai cewa rushewar ta faru ne da safiyar Juma’a, inda ta shafi wani ɓangare na rumfar shiga ginin (entrance canopy) da ake ginawa.
- Zama Ɗan Ƙasa na Jos ta Arewa: Kotu Ta Dage Shari’ar Ɗaukaka Ƙara Zuwa 29 Ga Oktoba
- An ceto ɗaliban Oyo bayan shafe watanni biyu a hannun masu garkuwa
- ‘Yan Sandan Abuja sun ceto mutane huɗu da aka yi garkuwa da su bayan musayar wuta da masu garkuwa
A cewarsa, ma’aikata biyar na karɓar magani a Asibitin Kwararru na Jihar Gombe, yayin da wasu biyu ke samun kulawa a Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Gombe.
Ya ƙara da cewa, mutum ɗaya ya mutu sakamakon hatsarin.
Tuni dai gwamnatin jihar ta umurci Ma’aikatar Ayyuka tare da hukumomin da abin ya shafa da su fara aiwatar da bincike kan musabbabin afkuwar lamarin.