Kyaftin Din argentina, Lionell Messi

Kocin Argentina Lionel Scaloni ya ce bai yi mamaki ba kan yadda Lionel Messi ke da shekaru 39, kuma har yanzu ke taka leda me kyau.

Scaloni, wanda ya jaddada hakan ranar Jumma’a, ya ce yana ganin kyaftin ɗin zai iya kasance mafi kyawun ɗan wasa a duniya muddin yana son ci gaba da buga wasa.

“Ba ya ba ni mamaki ko kadan,” in ji shi.

“Wataƙila mutanen da ba su san shi ba ne ke yin mamakin shekarunsa 39 kuma har yanzu ya na buga wasa da kyau.”

Argentina za ta fafata da Switzerland a wasan kwata-fainal ranar Asabar a Kansas City. Scaloni ya yaba da abokan karawarsu, wadanda suka kai matakin wasan kwata-fainal a karon farko cikin shekaru 72.

“Babu abokin karawa mai sauƙi, duk mun san haka,” in ji Scaloni.

Idan Argentina ta doke Switzerland, za ta fafata da Ingila ko Norway a wasan kusa da na ƙarshe.

Messi ya taka rawa sosai a ƙoƙarin da Argentina ke yi don sake lashe Gasar Kofin Duniya, inda ya ci ƙwallaye 8 a wasanni 5, kuma yanzu shi ne wanda ya fi kowa cin ƙwallo a tarihin Gasar Kofin Duniya, da kwallaye 21.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *