Nasarawa Amazons na murnan lashe kofin da ta dauka.

Nasarawa Amazons ta lashe Gasar Shugaban Ƙasa ta Tarayya ta Mata ta bana 2026, bayan doke Heartland Queens da ci 6-5 a bugun fenareti bayan an tashi wasa a cikin fili ci 1-1.

Wasan ya gudana ne a Filin wasa na Stephen Keshi da ke Asaba, ranar Asabar, a gaban magoya baya da kuma masu rike da madafan iko a al’amurar ƙwallon ƙafa.

Chizoba Johnson ce ta fara zura wa Heartland Queens ƙwallo bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, kafin Adaobi Judith wadda ta shigo daga benci ta rama wa Nasarawa Amazons.

Bayan bugun fenaretin, magoya bayan tawagar Nasarawa Amazons sun kasance cikin farin ciki da murna da kuma rera waƙa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *