Ɗan wasan Bafana Bafana mai taka leda a ƙungiyar Mamelodi Sundowns, Jayden Adams ya riga mu gidan gaskiya.
Ɗan wasan ya rasu ne yana da shekaru 25 bayan dawowa daga wakiltar Afirka ta Kudu a Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026.
Marigayin ya taka muhimmiyar rawa ma Bafana Bafana a wasannin rukuni na Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026, inda ya taimaka wa ƙasar ta kai zagaye na 32.
-
Nasarawa Amazons ta lashe Gasar Shugaban Ƙasa ta Tarayya ta Mata ta 2026
-
Gasar Cin Kofin Mata na Afirka: Madugu ya gayyaci Ajibade da Oshoala
-
Gasar Cin Kofin Duniya 2026: Rice da Guehi da James na Ingila sun yi artisaye kafin haɗuwar su da Norway
Iyalansa da ma ƙungiyarsa ta Mamelodi tuni suka tabbatar da rasuwar da safiyar ranar Asabar.
Al’umma da ma Gwamnatin ƙasar sun bayyana alhininsu game da wannan rashi a cikin sanarwar da ƙasar ta fitar.