Mahaifin Sarkin Qatar na yanzu, Sheikh Hamad bin Khalifa Al Thani, ya rasu sanar.da shekaru 74 a duniya, kamar yadda fadar masarautar Qatar (Amiri Diwan) ta sanar

Sanarwar fadar ta ce: “Da zukatanmu cike da imani da hukuncin Allah da kaddararsa, Amiri Diwan na jimamin babban rashi da al’umma ta yi na rasuwar Mai Martaba Uban Sarkin Qatar Sheikh Hamad bin Khalifa Al Thani – Allah ya ji kansa – wanda ya rasu da safiyar yau Lahadi.”

Qatar ta ayyana zaman makoki na tsawon kwanaki hudu daga ranar Litinin, inda aka dakatar da ayyuka a hukumomin gwamnati da sauran cibiyoyin jama’a, sannan aka saukar da tutocin ƙasa zuwa rabin sandar tutatuta.

Sheikh Hamad, wanda ya mulki Qatar daga shekarar 1995 zuwa 2013, ya kasance daya daga cikin manyan wadanda suka tsara ci gaban Qatar a zamanance.

A lokacin mulkinsa, kasar ta samu gagarumin ci gaba ta fuskar tattalin arziki da zamantakewa da al’adu, lamarin da ya kara mata matsayi a idon duniya.

Sheikh Hamad ya jagoranci manyan ayyukan zuba jari da tattalin arziki tare da kulla yarjejeniyoyi da kasashe daban-daban, yayin da Qatar ta zama kasa mafi girma wajen fitar da iskar gas (LNG) zuwa kasashen duniya.

A shekarar 2022, Qatar ta karbi bakuncin gasar cin kofin duniya ta FIFA, wadda ita ce babbar gasar kwallon kafa da aka fi kallo a duniya.

Sheikh Hamad ya samu yabo da tafi daga magoya baya a lokacin bude gasar.

A lokacin mulkinsa ne aka kafa tashar talabijin ta Al Jazeera a shekarar 1996, wacce ta zama daya daga cikin manyan kafafen yada labarai masu tasiri a duniya.

Har ila yau, a zamaninsa ne aka samar da kundin tsarin mulkin Qatar na farko na dindindin a shekarar 2004, tare da gabatar da zabukan kananan hukumomi, inda aka bai wa mata damar kada kuri’a da kuma tsayawa takara.

A shekarar 2013, Sheikh Hamad ya mika mulki ga dansa kuma magajinsa, Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani, wanda a lokacin yake da shekaru 33.

Wannan ya kasance wani abu da ba kasafai ake gani ba a tsakanin sarakunan kasashen Larabawa na yankin. Gulf.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *