Matashin dan wasan Najeriya, Zadok Yohanna, ya shiga cikin jerin sunayen ‘yan takara 100 na kyautar golden boy ta 2026.
A cikin jerin sunayen da aka fitar, matashin yana matsayi na 80 a fafatawar neman kyautar da aka kebe wa ‘yan wasan da ba su wuce shekaru 21 ba a Turai.
Jaridar wasanni ta kasar Italiya mai suna Tuttorsport ce ke gabatar da wannan kyauta kowace shekara tun daga 2003.
- Ɗan wasan Afirka ta Kudu Jayden Adams ya rasu bayan dawowa daga Gasar Cin Kofin Duniya
- Golden eaglets ta kammala gasar China da kunnen doki da masu masaukin baƙi
- Nasarawa Amazons ta lashe Gasar Shugaban Ƙasa ta Tarayya ta Mata ta 2026
Ana bai wa dan wasa mafi fice da bai wuce shekaru 21 kuma yana buga kwallo a daya daga cikin manyan Gasar Turai da UEFA ta amince da su.
Kungiyar manyan ‘yan jaridun kwallo ce ke zabar wanda zai lashe kyautar.
A kwanan nan Zadok ya koma kungiyar Brighton & Hove Albion na Ingila daga AIK stockholm na Sweden, inda ya sanya hannu kan kwantiragin shekaru biyar wanda zai kare a watan yuni na 2031.
Zadok ya fara buga kwallo a kungiyar Ikon Allah football academy a Najeriya, kafin ya koma Sweden a 2025 ya shiga AIK, inda ya yi saurin koyan salon taka leda na kasar Turai.
A wannan kaka, ya buga wasanni 18 da AIK, inda ya zura kwallaye 5 ya kuma bayar da taimakon cin kwallo 4.