Dakarun Operation HAƊIN KAI sun ce sun daƙile wani yunƙurin mayaƙan ƙungiyar ISWAP na kutsawa garin Cross Kauwa da ke Ƙaramar Hukumar Kukawa a Jihar Borno, inda suka yi wa ‘yan ta’addan mummunar ɓarna tare da tilasta musu tserewa.
A cikin wata sanarwa da Laftanar Kanar Mohammed Goni ya fitar, an bayyana cewa harin ya faru ne da misalin ƙarfe 10:20 na dare a ranar 11 ga Yulin 2026, lokacin da mayaƙan ISWAP suka yi ƙoƙarin kutsawa sansanin dakarun Brigade ta 19 da ke ƙarƙashin Sashe na 3 na Joint Task Force North East, Operation HAƊIN KAI.
Bayan artabun, dakarun sun ce sun kashe wani ɗan ta’adda mai ɗaukar bidiyo tare da ƙwato wata kyamarar Sony Camcorder da ke ɗauke da bayanan ayyukan ƙungiyar da bidiyoyin farfaganda.
- Sojojin Bataliya ta 65 sun kama motar da ke ɗauke da manyan miyagun ƙwayoyi a hanyar Lagos zuwa Calabar
- An ceto ɗaliban Oyo bayan shafe watanni biyu a hannun masu garkuwa
- Dakarun Operation HADIN KAI sun daƙile yunƙurin kutse da ISWAP ta yi a Borno
Sanarwar ta ƙara da cewa binciken farko kan bayanan da ke cikin ƙyamarar ya nuna cewa wasu manyan kwamandojin ISWAP guda huɗu ne suka jagoranci harin, tare da haɗin gwiwar wasu mutane uku daga ƙasashen waje.
An bayyana sunayen biyu daga cikinsu a matsayin Abu Ishaq, wani Bafalasɗine da ake zargin shi ne babban mai horas da mayaƙan ISWAP da Abu Thaiba, wani ɗan ƙasar Morocco wanda aka ce likita ne a cikin ƙungiyar.
Haka kuma, rundunar ta ce akwai wani Balarabe na uku da har yanzu ba a gano ko wanene ba.
Sanarwar ta ce hotunan tauraron ɗan adam da bayanan sirri sun nuna cewa ‘yan ta’addan sun kwashe gawarwakin wasu daga cikin mayaƙansu yayin da suke ja da baya, yayin da wasu da dama suka samu raunukan harbin bindiga.
Sai dai sojoji biyu suma sun samu raunuka a yayin musayar wutar.
An ce an kwashe su ta jirgin sama domin ci gaba da jinya, kuma su na ci gaba da samun lafiya.