Wata kotu da ke birnin Port Sudan, wanda ke ƙarƙashin ikon rundunar sojin Sudan, ta yanke wa shugaban rundunar RSF, Mohamed Hamdan Daglo, da wasu mutum 15 hukuncin kisa ba tare da sun bayyana a gaban kotu ba.

An dai zargi Daglo da kashe gwamnan wata jiha da kuma aikata laifukan yaƙi a yankin Darfur, kamar yadda kafafen yaɗa labaran gwamnati suka ruwaito.

Wannan hukunci, wanda kotun da ke aiki ƙarƙashin gwamnatin soji ta yanke, shi ne na farko da aka yanke kan manyan shugabannin RSF tun bayan ɓarkewar yaƙi tsakanin rundunar da sojojin Sudan a watan Afrilun shekarar 2023

Kamfanin dillancin labaran gwamnati na SUNA ya ce kotun ta sami Daglo da sauran waɗanda ake tuhuma da laifukan yaƙi da laifukan cin zarafin bil’adama da kisan kare dangi (genocide), da kuma kai hare-hare kan fararen hula da cibiyoyin gwamnati.

Waɗanda aka yanke wa hukuncin sun haɗa da ƙanin Daglo kuma mataimakinsa, Abdelrahim Hamdan Daglo, da wasu jami’an RSF da kuma wasu shugabannin ƙabilun Larabawa daga yankin Yammacin Darfur.

Shari’ar ta ta’allaka ne kan kisan gwamnan Jihar Yammacin Darfur, Khamis Abbakar, a watan Yunin shekarar 2023, jim kaɗan bayan da dakarun RSF suka ƙwace iko da birnin El-Geneina, babban birnin jihar.

An kashe Abbakar ne sa’o’i kaɗan bayan ya zargi RSF da ƙungiyoyin da ke mara mata baya da kai hare-hare kan fararen hula.

Shugaban rundunar sojin Sudan, Abdel Fattah al-Burhan, da Mohamed Hamdan Daglo sun kasance tare wajen jagorantar juyin mulkin shekarar 2021, wanda ya dakatar da shirin miƙa mulki ga gwamnatin farar hula.

Sai dai daga baya suka samu saɓani kan shirin haɗa rundunar RSF cikin rundunar sojin ƙasa, rikicin da daga bisani ya rikide zuwa yaƙi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *