Dakarun Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Gabas, Operation HADIN KAI (OPHK), sun daƙile wasu hare-haren kutse da mayaƙan ƙungiyar ISWAP suka yi ƙoƙarin kai wa a wurare daban-daban na Jihar Borno a safiyar Juma’a.
A cewar sanarwar da Muƙaddashin Jami’in Yaɗa Labaran rundunar, Kyaftin Mohammed Goni, ya fitar, ‘yan ta’addan sun yi yunƙurin kutsawa ta yankunan Muna Garage, ƙauyen Shuwari da kuma Ajilari Cross tsakanin ƙarfe 12:20 na dare zuwa 2:30 na dare, da nufin shiga cikin birnin Maiduguri.
Sanarwar ta ce dakarun sun gano motsin ‘yan ta’addan ne tun da wuri sakamakon ingantaccen tsarin tattara bayanan sirri da rundunar ta tanada, inda suka buɗe musu wuta daga wurare daban-daban, lamarin da ya dakile duk wani yunƙurin kutsawar.
- Mayaƙan ISWAP da iyalansu sun miƙa wuya – Sojoji
- Za mu cigaba da matsa ƙaimi a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya-Waidi Shuaibu
- Sojoji sun daƙile harin ISWAP kan sansanin Logomani
Haka kuma, sojojin sun ce sun daƙile wasu ƙarin yunƙurin kutsawa da ‘yan ta’addan suka yi a yankunan Miringa da Dutsen Kura da ke Buratai.
A yayin da sojoji ke bin sawun ‘yan ta’addan da suka tsere a Miringa, wata motar soji sulke (MRAP) ta taka wata na’urar fashewa da aka binne a ƙasa (IED).
Sai dai sanarwar ta tabbatar da cewa babu wani soji da ya jikkata sakamakon fashewar, tare da cewa al’amura na ci gaba da kasancewa cikin kwanciyar hankali.
Rundunar ta yi kira ga jama’a da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanan sirri domin tallafa wa ƙoƙarin yaƙi da ta’addanci.