Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa, (NEMA), ta bayyana cewa jihohi 33 na Najeriya na fuskantar barazanar ambaliyar ruwa a daminar bana.
Babbar Daraktar hukumar, Hajiya Zubaida Abubakar Umar, ta bayyana hakan yayin wata ziyarar ban girma da ta kai wa Shugaban Hafsan Sojojin Ƙasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu, a Abuja.
Ta ce hukumar na shirin gudanar da atisayen gwaji a jihohin Oyo da Cross River da Adamawa domin tantance yadda za a tunkari yiwuwar ambaliyar ruwa.
- Sojoji sun kama wata da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi ga ‘Yan Ta’adda a Tafkin Chadi
- Gwamnatin Zamfara ta amince da hutun haihuwa na watanni 6 ga mata ma’aikata
Zubaida ta yaba wa Rundunar Sojin Ƙasa bisa gudunmawar da take bayarwa a ayyukan ceto da agajin gaggawa, tare da neman ƙarin tallafi musamman a fannonin aikin injiniya, da jiragen sama da ayyukan bincike da ceto.
Ta ce haɗin gwiwar hukumar NEMA da Rundunar Sojin Ƙasa zai ƙara ƙarfafa shirin ƙasar na rage asarar rayuka da dukiyoyi sakamakon iftala’i.