Isra’ila ta bai wa Amurka bayanan sirri da ke nuna cewa akwai wani zargin sabon shiri daga Iran na kashe Shugaban Amurka, Donald Trump.
Rahotanni sun ce bayanan da Isra’ila ta miƙa sun ƙunshi cikakkun bayanai kan abin da ta bayyana a matsayin shirin kai hari kan Trump.
Sai dai jami’an leƙen asirin Amurka sun ce har yanzu ba su tabbatar da sahihancin waɗannan bayanan ba.
- Yarjejeniya – Amurka da Iran sun ƙara kai wa juna hare-hare
-
Yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin mu da Iran ta Rushe — Trump
Fadar White House ta yi nuni da kalaman Trump, inda ya ce Iran na ci gaba da ƙoƙarin kai masa hari, yana mai zargin Tehran da ɗaukar fansa kan kisan tsohon kwamandan sojin Iran, Qasem Soleimani, a shekarar 2020.
Sai dai wasu jami’an leƙen asirin Amurka sun yi gargadin cewa ya kamata a yi taka-tsantsan wajen kallon bayanan Isra’ilar, saboda hakan zai iya kasancewa wani ɓangare na ƙoƙarin rinjayar manufofin Washington kan Iran.
Lamarin na zuwa ne yayin da rikicin Amurka da Iran ke ci gaba da ƙamari, duk da cewa ana ci gaba da tattaunawar neman cimma sabuwar yarjejeniyar shirin nukiliyar Iran.
