Trump ya zargi Iran da kwan gaba kwan baya a tattaunawar tsagaita wuta

Shugaban Amurka Donald Trump ya zargi Iran da ɗaukar tsawon lokaci suna sauya ma’anar abubuwan da aka cimma a yarjejeniyar tsagaita wuta da aka rattaɓa wa hannu a ranar 17 ga watan Yunin shekarar 2026.

A ranar Laraba ne Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa yarjejeniyar tsagaita wuta da Iran “ta zo ƙarshe” biyo bayan munanan hare-haren da aka yi ta musayar su tsakanin dakarun Amurka da na Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Washington ta kai jerin hare-hare cikin daren Talata a Jamhuriyar Musulunci ta Iran, yayin da majiyar dakarun juyin juya halin Iran ke cewa sun kai makamantan hare-hare kan sansanonin Amurka da ke yankin Gulf.

“Kowa ya amince cewa babu maganar makamin nukiliya a yarjejeniyar da muka ƙulla, amma suna fitowa sai su ka riƙa shaida wa manema labarai cewa ba mu ma taɓa tattaunawa a kai ba, kaga kenan akwai matsala tattare da su,” in ji Trump.

Rushewar yarjejeniyar, ta jefa fargaba a kasuwannin duniya, musamman ta fuskar samar da man fetur daga yankin Gulf, wanda hakan ya sa farashin ɗanyen mai ya tashi da kashi 5% cikin sa’o’i kaɗan bayan kalaman na Trump.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *