Babban kocin ƙasar Masar, Hossam Hassan, ya zargi hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya (FIFA) da jami’an wasa da nuna son kai ga zakarun gasar, wato ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta ƙasar Argentina, biyo bayan rashin nasara mai ban takaici da ƙasarsa ta yi da ci 3-2 a zagaye na ‘yan 16.

Masar ta bari an biya ta ƙwallaye biyu da take gaba da su a ranar Talata, yayin da Argentina ta yi babban bajinta ta dawo cikin wasan, ƙarƙashin jagorancin Lionel Messi, wanda ya taimaka aka ci ƙwallo ɗaya kuma shi da kansa ya zura ƙwallon da ta daidaita wasan, kafin Enzo Fernández ya zura ƙwallon nasara a lokacin da aka ƙara na rauni.

‘Yan wasan Masar sun fita cikin takaici bayan da aka soke musu ƙwallo ɗaya biyo bayan duba na’urar taimaka wa alƙalin wasa (VAR), yayin da jami’an wasan suka ƙi duba wani lamari da suke gani kamar an yi wa Mohamed Salah laifi ne ta hanyar yi masa ƙeta da Alexis Mac Allister ya yi, kafin Argentina ta tafi ta ci ƙwallon nasara.

Da yake magana bayan kammala wasan, Hassan ya yi zargin cewa wasu abubuwa na daban sun yi tasiri ga sakamakon wasan.

“Wataƙila suna so su sayar da zakaran duniyar a gasar. Wataƙila suna so Messi ya ci gaba da kasancewa a gasar. A ƙwallon ƙafa, wani lokacin akwai abubuwan waje da suka wuce batun fasahar wasa. Zakaran duniyar ya sami tallafi ta kowane mataki,” in ji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *