Ƙungiyar Likitoci Masu Zaman Kansu ta ƙasa da ƙasa (MSF/Doctors Without Borders) ta bayyana cewa ta kammala aikin jiyyar gaggawa na cutar Mashaƙo (diphtheria) a Jihar Kano, bayan da ta gudanar da allurar rigakafi ga yara fiye da 835,000.
Ƙungiyar agajin ta jiyya ta bayyana cewa wannan tallafi ya kawo ƙarshen ayyukan tallafawa na tsawon shekaru uku da ta yi a lokacin da aka fuskanci ɗaya daga cikin mafi girman ɓarnar cutar makwallato da aka taɓa samu a tarihin Nijeriya.
Haka kuma, ta bayyana cewa ta yi aiki ne tare da Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano, inda suka gudanar da manyan kamfen ɗin rigakafi sau biyu tsakanin watannin Afrilu da Yuni na shekarar 2026.
A zagayen farko sun isa ga yara 348,080, yayin da a zagaye na biyu kuma suka kai ga yara 486,948 a faɗin mazabu 20.
- Hukumar kula da Jami’an Ƴan Sanda ta Ƙasa (PSC) ta amince da korar manyan jami’an ‘ƴan sanda 4 daga aiki.
- Obi ya kafa tarihi a fagen siyasar Arewa’-Kwankwaso
- Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin bincikar Hukumar nan ta bogi
Gudanar babban aikin na MSF a Kano, Abdoul Aziz Djibrilla, ya bayyana cewa ɓarnar cutar ta jefa iyalai da cibiyoyin lafiya cikin matsin lamba na gaske, inda aka riƙa kwantar da yara fiye da 100 kowace rana a lokacin da cutar ta tsananta tsakanin ƙarshen shekarar 2025 zuwa farkon 2026.
Ya ce :”Ko da yake an sami raguwar mace-mace da kamuwa da cutar a ‘yan watannin nan, musamman saboda kamfen ɗin allurar rigakafi na bai-ɗaya, cutar makwallato tana ci gaba da kasancewa babbar barazana ga lafiya sakamakon ƙarancin yaduwar allurar rigakafi na yau da kullum, cunkoson jama’a, jinkirin neman magani, da kuma matsalar rashin abinci mai gina jiki,” in ji shi yana mai gargaɗi.
Ya ƙara da cewa, tun lokacin da aka fara bayar da agajin a shekarar 2023, kungiyar MSF ta yi jiyyar yara 14,707 a cibiyoyin jiyyarta da sauran wuraren da take tallafawa, yayin da kuma ta ƙarfafa tsarin tura marasa lafiya (referral), sa ido kan cututtuka, da kuma haɗa kai da al’umma.
A cewar Ma’aikatar Lafiya ta Jihar, jihar ta yi rajistar mutane 31,900 da ake zargin sun kamu da cutar, yayin da aka samu mace-mace fiye da 1,260 tsakanin watan Maris 2022 zuwa Maris 2026.
Wannan ya wakilci babban kaso na adadin mutane 65,759 da ake zargi sun kamu da cutar da kuma mace-mace 2,229 da hukumar NCDC ta gudanar da rahotonsu a fadin ƙasar baki ɗaya.