Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya umarci Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) ta gudanar da cikakken bincike kan wata Hukuma da ke kiran kanta “Presidential Foreign Intervention Promotion Council (PFIPC)”.
Fadar shugaban ta ce hukumar ba ta da tushe a dokance, kuma babu kowanne irin umarni daga shugaban ƙasa wajen kafa ta.
Sanarwar ta ce wani mutum mai suna Adeniyi Adeyemi Mathew ya riƙa gabatar da kansa a matsayin Darakta Janar na Hukumar ta bogi, bisa iƙirarin cewa shugaban ƙasa ne ya naɗa shi.
Ana zargin sa da amfani da takardun gwamnati na bogi domin neman amincewa daga hukumomin gida da na waje, ciki har da samar da biza.
-
An samu ce-ce-ku-ce a Kaduna bayan bazuwar sautin murya da ake dangantawa da Isa Ashiru
-
Najeriya ta bayyana alhinin kisan ‘yar ƙasar a Ukrain
Fadar shugaban ƙasa ta ce binciken zai kuma haɗa da gano yadda aka buɗe wasu asusun banki da sunan Hukumar, da kuma bibiyar asalin kuɗaɗen da suka shiga ko suka fita ta waɗannan asusun.
Shugaba Tinubu ya kuma umarci ICPC ta gano duk wani gurbi da ke cikin tsarin gudanarwar gwamnati da aka yi amfani da shi wajen aiwatar da wannan zargi, tare da ba da shawarwarin matakan gaggawa da za su hana sake faruwar irin haka anan gaba.
Haka nan ya umarci dukkan ma’aikatu, hukumomi da ofisoshin gwamnatin tarayya su bai wa ICPC cikakken haɗin kai da duk bayanan da take buƙata domin kammala binciken cikin gaggawa.
Shugaban ya jaddada cewa dole ne a kare martabar fadar shugaban ƙasa da ta gwamnatin tarayya daga masu yin sojan gona, jabun takardu da amfani da sunan gwamnati ba bisa ƙa’ida ba.
Ya kuma umarci cewa duk wanda bincike ya tabbatar da laifinsa a hukunta shi bisa tanadin doka.
Shugaban ya kuma baiwa hukumar wa’adin kwanaki 30 ta kammala bincike, tare da miƙa masa cikakken rahoto.
