Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana rashin jin daɗin sa game da hirar da tsohon Gwamnan Jihar Borno, Sanata Ali Modu Sheriff, ya yi da gidan talabijin ta Channels TV a ranar Litinin da ta gabata, inda ya soki kalaman Sheriff ɗin a matsayin waɗan da ba su dace ba.
Kwankwaso ya bayyana cewa, bayan dogon lokaci da Sheriff ya yi bai fito fili yana magana kan al’amuran ƙasa ba, ana tsammanin zai dawo da kyakkyawan tunani, sai dai abin takaici kalaman na sa sun nu na akasin haka.
A cikin hirar tasa, Ali Modu Sheriff ya yi ikirarin cewa ɗan takarar shugaban ƙasa, Peter Obi, ba zai iya samun gagarumin goyon baya a yankin Arewacin Najeriya ba.
Kwankwaso ya mayar da martani da cewa abin mamaki ne yadda Sheriff ya naɗa kansa a matsayin mai magana da yawun talakawan Arewa.
‘Obi Ya Kafa Tarihi A Arewa’
Kwankwaso ya tunatar da Sheriff cewa, a fafatawar sa ta farko a zaɓen shugaban ƙasa, Obi ya samu kusan ƙuri’u miliyan 2.8 a yankin Arewa kaɗai, wannan babbar nasara ce da ba za a iya gogawa da shi cikin sauƙi ba.
Ya ƙara da cewa, idan aka yi la’akari da halin matsin rayuwa da ƙasar ke ciki, da kuma ittifakin da ƴan Najeriya suka yi kan gazawar gwamnatin APC, haɗakar tikitin “OK” (Obi-Kwankwaso) wanda ke ɗauke da jigon siyasar Arewa da shi kansa ya taɓa samun ƙuri’u miliyan 1.45 a yankin, ya nuna cewa tikitin na ci gaba da kasancewa babbar barazana ga kowacce irin rundunar siyasa a Arewa.
Matsayar Mutanen Kano Kan Siyasa
Dangane da ikirarin Sheriff na cewa mutanen jihar Kano ba za su zaɓi Peter Obi ba, Kwankwaso ya fito fili ya nuna ba haka maganar ta ke ba.
“Mutanen Kano ba masu nuna kyama ko banbanci ba ne. Sun daɗe suna nuna tsantsar amincewar su da tafiyar Kwankwasiyya, kuma za su marawa kowane nagartaccen ɗan takara baya da aka fito da shi ƙarƙashin inuwar wannan tafiya.” Inji Kwankwaso.
Daga ƙarshe, Kwankwaso ya baiwa tsohon gwamnan shawarar, a duk lokacin da zai sake bayyana a gidajen talabijin, ya mayar da hankali kan matsalolin tsaro da na matsin rayuwa da suka addabi jihar sa ta haihuwa (Borno), maimakon yin kalaman da ke raba kan al’umma.
