Hukumar kula da Jami’an Ƴan Sanda ta Ƙasa (PSC) ta amince da korar manyan jami’an ƴan sanda guda huɗu daga aiki.
Cikin wata sanarwa da Jami’in da hulɗa da Jama’a na Hukumar, Torty Njoku Kalu ya fitar a ranar Talata, jim kaɗan bayan kammala babban taron hukumar a Abuja, Hukumar ta ce ta yiwa ƙarin jami’ai 31 gargaɗi, bayan samun su da laifukan da suka saɓa da ka’idojin aikin Ɗan Sanda.
Sanarwar tace an kuma rage wa ƙarin jami’ai huɗu matsayi, uku daga ciki sun sauka daga matsayin Sufuritanda (SP) zuwa Mataimakin Sufuritanda (DSP).
Har ila yau, an rage wa ƙarin jami’ai biyu matsayi daga Mataimakin Sufuritanda (DSP) zuwa Assistant Sufuritanda (ASP).
Sai kuma ƙarin wasu jami’ai biyar, da su ma aka rage musu girma daga muƙamin ASP zuwa matsayin Sufeto (Inspector)
Hukumar ta bayyana cewa, ta tilasta wa wasu jami’ai biyu ritaya da wuri domin kaucewa haɗarin da suke da shi ga Al’umma.
Rundunar, ta kuma raba wasu takardun gargadi da tsawatar wa ga jami’ai da dama, inda 10 daga ciki suka sha gargaɗin ƙarshe, biyar kuma aka yi musu gargaɗin gyaran hali, uku kuma aka ba su wasiƙun kashedi, sannan jami’i ɗaya aka ba shi wasiƙar shawara.
Sai dai kuma, a taron hukumar an wanke jami’ai bakwai bayan da bincike ya nuna ba su da laifi.
Sanarwar ta sake jaddada aniyar hukumar na dawo da karsashi da kiyaye ƙa’idojin aiki, da kuma sake farfaɗo da martabar Rundunar Ƴan Sandan Najeriya a idon Al’umma.
