Argentina ta samu nasarar kai wa ga matakin kwata fainal, bayan ta doke takwararta ta Masar da ci 3-2.
A zagayen farko na wasan, Masar ce ta samu nasarar zura ƙwallo guda, har lokacin da Argentina ta samu bugun daga kai sai mai tsaron gida, inda Messi ya zubar.
Haka aka kai ƙarshen wannan zagaye na farko, Argentina ba ta samu damar farke wannan ƙwallon ba.
- Hukumar Almajirai ta musanta zargin da aka yi mata na gina sabbin tituna – Copy
- Manyan kwamandojin ‘yan ta’adda sun miƙa wuya
- Hukumar Almajirai ta musanta zargin da aka yi mata na gina sabbin tituna
Dawowar wasan a zagaye na biyu ke da wuya, Masar ta sake samun damar jefa ƙwallo ta biyu a ragar Argentina, inda aka alƙalin wasa ya hana ƙwallon.
A cikin mintuna saba’in da doriya da take wasan ne, Argentina ta samu nasarar saka ƙwallon farko a ragar Masar da tallafin ɗan wasan ta Lionel Messi.
Daga nan ne fa salon wasa ya sauya, inda cikin ‘yan mintuna kaɗan, Argentina ta sake jefa ƙwallo ta biyu ta hannun Messi.
Kamar dabo, sai ga shi a ‘yan mintuna kaɗan kafin a busa usur na ƙarshe, Argentina ta sake zura wa Masar ƙwallo ta uku, wanda aka tashi da ci 2-3
Yanzu haka ɗan wasa Lionel Messi ya na da ƙwallaye 8 cif-cif da ya zura a raga a wasannin da ƙasar sa ta buga a Gasar cin Kofin Duniya da ake bugawa a bana.