Rundunar Operation Hadin Kai ta sanar da cewa wasu manyan kwamandojin ‘yan ta’adda biyu sun miƙa wuya ga dakarun ta a yankin Geidam na Jihar Yobe, lamarin da ta ce na ƙara nuna raunin ƙungiyar ke samu a Arewa maso Gabas.

A cewar rundunar, waɗanda suka miƙa wuya sun kasance daga cikin manyan shugabannin ƙungiyar, kuma sun isa Maiduguri a ranar 5 ga Yuli, inda a yanzu suke hannun sojoji domin gudanar da bincike da tattara bayanan sirri.

Rundunar ta ce bayanan farko da ta samu daga wajen su, akwai  muhimman bayanai kan yadda ‘yan ta’addan ke gudanar da hare-harensu, hanyoyin samun kayan aiki da tsarin shugabancinsu.

Ta ƙara da cewa ana sa ran wannan zai taimaka wajen gano tare da lalata sauran maɓoyar ‘yan ta’addan da suka rage a yankin.

Operation Hadin kai ta bayyana cewa ci gaba da matsin lambar da dakarun ta ke yi ta ƙasa da sama, da haɗin gwiwa da sauran jami’an tsaro, na ci gaba da raunana ƙarfin ‘yan ta’addan, lamarin da ke sa wasu daga cikinsu miƙa wuya.

Rundunar ta kuma jaddada aniyar ta na ci gaba da kai hare-hare, har sai an kawar da duk wata barazanar ta’addanci tare da dawo da zaman lafiya mai ɗorewa a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *