Waidi Sha'aibu ya bukaci kafafen yada labarai su tallafawa Rundunar sa wajen yaki da labaran karya

Babban Hafsan Sojin Najeriya Laftanar Janar Waidi Sha’aibu, ya ce yaɗa labaran ƙarya da farfaganda na haifar da barazana ga tsaro, lamarin da ke nuna buƙatar ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin sojoji da kafafen yaɗa labarai.

Shaibu ya bayyana hakan ne a ranar Talata a Abuja yayin buɗe Taron karawa juna sani da sashen Hulɗa da Jama’a na Rundunar Sojin Kasa (DAPR) ya gudanar.

Waidi Sha’aibu wanda ya samu wakilcin Babban Jami’in shiga tsakanin Soji da Fararen Hula, Manjo Janar Musa Etsu-Ndagi, ya ce maƙiya a wannan zamani na amfani da yaɗa bayanan ƙarya da dabarun yaƙi domin yaudarar jama’a.

Ya bayyana cewa ingantacciyar hulɗa da kafafen yaɗa labarai ta zama wata muhimmiyar hanya da ke ƙara ƙarfi ga ayyukan tsaro na haɗin gwiwa tsakanin hukumomi daban-daban.

A cewarsa, ya kamata a fahimci cewa maƙiya na dogaro sosai da farfaganda da karkatar da bayanai.

“Idan ba a dakile yaɗa bayanan ƙarya ba, zai iya yin illa kamar yadda wata barazana ta tsaro kai tsaye za ta yi.”-Inji Manjo Etsu-Ndagi

Ya ce yanayin tsaro da ke ci gaba da sauyawa na buƙatar haɗin gwiwa tsakanin sojoji da kafafen yaɗa labarai  da goyon bayan jama’a, anan ana bukatar ingantacciyar sadarwa da zata  taimaka wajen kyautata haɗin kai tsakanin rundunar da al’umma.

Ya bayyana cewa kafafen yaɗa labarai sun wuce sanar da jama’a halin da ake ciki kawai, sun zamanto wata hanyar fadakarwa da fahimtar da jama’a sahihan bayanai domin kawar da labarai na ƙarya.

A karshe yayi fatan taron zai samar da damar musayar ra’ayi, da buɗe ingantattun hanyoyin bayar da rahotanni masu alaka da rikice-rikice, da kuma samar da dabarun yaƙar bayanai marasa tushe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *