Tsohon Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) Kingsley Moghalu, ya danganta gwagwarmayar kwatar kai da Najeriya ke ciki daga ta’addanci da gazawar ‘yan kasar ta fuskar kishi da kaunar juna.
Da yake magana a wani shiri na tashar talabijin ta ARISE, Moghalu ya bayyana cewa gazawar ƙasar wajen samar da haɗin kai na siyasa, zamantakewa, ƙabila da tarihi ya raunana ƙoƙarin da take yi na magance matsalolin tsaro.
A cewarsa, ta’addanci na ci gaba da bunƙasa ne saboda yawancin ’yan Najeriya ba sa kallon matsalar a matsayin ta kowa da kowa, da ke buƙatar haɗin kai domin magance ta.
- An harbe wani Mutum a Abuja
- NLC Da TUC sun yi barazanar tsunduma yajin aiki
- An gano Matar da ta sace kanta a Otal
“Gazawar Najeriya wajen shawo kan ta’addanci ya samo asali ne daga gazawarta na zama cikakkiyar ƙasa. Ba ma kallon matsalolinmu a matsayin matsalolin da suka shafi kowa da kowa,” in ji Moghalu.
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar karkashin inuwar (YPP) ya ce ƙasashen da ke fuskantar barazana kan fi samun nasara wajen tattara al’ummarsu domin tunkarar matsaloli, idan jama’arsu na da zuciyar kishin ƙasa da manufa guda.
Ya bayyana cewa rarrabuwar kawuna da ke cikin Najeriya ta sa ya zama da wahala a samar da irin haɗin kan da ake buƙata domin yaƙar ƙungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi da sauran matsalolin tsaro.
Moghalu ya kuma yi nuni da yawan zarge-zargen haɗin baki tsakanin wasu jami’an tsaro da ’yan ta’adda a matsayin wata alama ta manyan ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta.
Kalaman Moghalu sun ƙara tayar da muhawarar da ake yi kan tushen matsalar rashin tsaro a Najeriya, inda masana da dama ke ganin cewa magance matsalar ba ta tsaya ga amfani da ƙarfin soja kaɗai ba, sai an haɗa da ƙarfafa cibiyoyin gwamnati, gina haɗin kan ƙasa da kuma tabbatar da shugabanci na adalci da bai wa kowa dama.
Najeriya ta shafe fiye da shekaru goma tana fama da matsalolin tada ƙayar baya, fashi da makami, garkuwa da mutane da sauran manyan laifuka, a yankunan Arewaci da sannu a hankali ke yaduwa zuwa sauran sassan kasar.
