An gano wata Matar Aure mai suna Oluchi a wani otal a Jihar Delta bayan ta yi karya cewa an sace ta kuma ta nemi Naira miliyan 50 daga iyalinta.

‘Ya’yan matar, ciki har da ‘yarta da ke kasar Kanada, sun roki jama’a da su taimaka musu wajen tara kudin, inda masu garkuwa da mutanen suka rage kudin fansan zuwa Naira miliyan 20.

‘Ya’yan matar sun shaida wa ‘yan sanda cewa an sace mahaifiyarsu a yankin Ikpoba Hill, da ke Karamar Hukumar Ikpoba-Okha ta Jihar Edo.

Sai dai binciken ‘yan sanda ya kai tawagar su ta musamman zuwa Jihar Delta, inda aka sami Matar da aka ce an sace tare da masoyinta a cikin Otal.

Wata majiya ta shaidawa Punch cewa, “ ‘Yan sanda sun gano lambar wayar namijin zuwa wani Otal a Ubiaroko, Jihar Delta. Inda suka tarar da shi da matar a wani Otal.

Majiyar ta kara da cewa, “Ofishin ‘Yan Sanda sun sanar da mijin matar halin da ake ciki kuma ya yi murna. Sai dai Matar ta roki mijin ka da ya fada wa ‘ya’yanta abin da ya faru.”

A wani faifan bidiyo da ya yadu a intanet, ‘yar matar mai suna Anita, da ke zaune a Kanada, ta ce abin da mahaifiyar su ta yi ya batawa iyalan su suna. Akan haka ta ce zasu bari doka tayi aikin ta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *