Kungiyoyin kwadago na Najeriya da suka hada da (NLC) da (TUC) sun sanar da cewa za su sake bude tattaunawar sabon mafi karancin albashi a watan Yuli na shekarar 2026.

Gamayyar kungiyoyin sun bayyana hakan ne a wani taron manema labarai, a wani bangare na taron kungiyar na duniya  karo na 114 a Birnin Geneva na kasar Switzerland.

Kungiyoyin kwadagon sun yaba da yadda gwamnonin jihohi suka fahimci cewa mafi karancin albashin Naira Dubu Saba’in da ake biya a yanzu, bai isa ya biya bukatun yau da kullum na ma’aikata ba.

Kungiyoyin sun bukaci gwamnonin da kada su yi gaggawar kayyade sabon mafi karancin albashi tukuna, su jira a bi hanyoyin da suka dace wajen gudanar da tattaunawa domin cimma matsaya guda.

Haka kuma, Gamayyar kungiyoyin na kwadago sun yaba da kokarin Gwamnatin Tarayya,  na dawo da biyan kudaden gratuti, inda suka bukaci gwamnati ta tabbatar da biyan duk wasu bashin kudaden ma’aikata na baya.

Idan za’a iya tunawa a ranar 18 ga watan Yuli na shekarar 2024 ne Shugaba Tinubu ya amince da biyan Naira Dubu Saba’in a matsayin mafi karancin albashi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *