A ranar Asabar, tsohon Shugaban masu rinjaye na Majalisar Dattawa kuma Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Ali Ndume, ya yaba wa Shugaba Bola Tinubu da Ministan Ayyuka, David Umahi, bisa fara sake gina da fadada titin Gombe zuwa Biu mai tsawon kilomita 125.

An kaddamar da aikin ne a ranar Alhamis 3 ga watan Mayu, wanda zai lankwame Naira Tiriliyan 1.245, a Garin Liji da ke Jihar Gombe.

Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, Ministan Ayyuka, David Umahi, da Manajan Darakta na Kamfanin Hi-Tech Construction, Danny Abboud, ne suka halarci taron.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja, Ndume ya bayyana aikin a matsayin cika alkawuran da gwamnatin Tinubu ta yi na gyara muhimman hanyoyin more rayuwa a Arewa maso Gabas.

“Aiki ne mai matukar amfani da zai bude damar tattalin arziki da inganta rayuwar ‘yan Najeriya,” a cewar Ndume.

Sai dai Sanatan ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta tsawaita aikin ya wuce Biu zuwa Maiduguri, Monguno, Ngala da Yola, don kara bunkasa kasuwanci, tsaro, da hadin kan yankin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *