Rahotanni daga masanaantar shirya Fina-Finan Hausa ta Kano (KannyWood) na bayyana cewa tauraruwa Ummi Ibro ta Amarce a karshen Mako.
Daya daga cikin Jaruman Masana’antar Ali Rabiu Ali (Daddy) ne ya sanar da hakan cikin wani sakon taya murna da ya wallafa a Shafin sa na Facebook.
Daddy ya bayyana cewa Ummi na daya daga cikin jaruman masana’antar da suka jima basuyi aureba, duk da sha’awar da ta dade tana nunawa na sha’awar shiga daga ciki.
Sai dai, Daddy ya danganta jinkirin auren nata da jinyar Mahaifiyar ta, wadda Allah ya karbi rayuwar ta daga bisani.
Da yake karin haske game da alakar Jarumar da sunan Marigayi Rabilu Musa Ibro, Daddy yace bawai ‘yar cikin sa bace, kawai dai sana’ace ta hada su.
“An sha rade-radin cewa ‘Yar gidan marigayi Rabilu Musa Ibro ce, amma a zahiri ba haka ba ne. Alaqar aiki ce ta hada ta da shi, kuma yayi mata halacci, shiyasa a lokacin da ake kiranta da Ummin Ibro, ba ta hana ba ko don shi ya ji dadi. Har Allah Ya dauki ransa.”
Rabi’u Ali Daddy ya ce bayyana Jarumar a matsayin mai riko da addini, wanda hakan ya bata gudunmuwa sosai yayin zamanta a masana’antar.
Sai dai ba safai Jaruman Masana’antar KannyWood kan bugi kirji tare da fitowa fili suna yabawa abokan sana’ar su ba, cikin wasu shirye-shairyen zantawa da wasunsu suka kirkiro a intanet, mafi yawa suna sukan juna ne.