Kungiyar Brighton & Hove Albion ta cimma yarjejeniyar daukar Zadok Yohanna daga AIK Stockholm kan kwantiragin shekaru biyar ba tare da bayyana kudin da aka biya ba.
Kocin Brighton, Hurzeler, ya ce yana farin ciki da daukar matashin dan wasan mai shekaru 18.
Kungiyar ‘Seagulls’ ta tabbatar da daukar dan wasan daga kungiyar AIK Stockholm ta Sweden kan kwantiragin shekaru biyar a ranar Asabar, inda Hurzeler ke da kwarin gwiwar cewa matashin zai karawa kungiyar karfi.
-
‘Yan wasan Arsenal Uku na takarar kyautar PFA a Ingila
-
Yamal ya lashe kyautar gwarzon dan wasan La Liga
“Ina fatan yin aiki da Zadok, bayan da na kalli wasanninsa da irin halayensa, shi dan wasa ne da zai iya yin tasiri a wasanni a ɓangaren gaba.” Inji Hurzeler
Kocin na Brighton ya ce kungiyar su za ta rabauta da halaye da nagartar Zadok, wanda zai zama wani babban ginshiki ga zabin sabbin ‘yan wasa anan gaba.
Yanzu haka, Brighton na da ‘yan wasan Najeriya guda biyu, da suka hadar da Mai tsaron ragar Kulob din mata Chiamaka Nnadozie, sai kuma sabon dan wasan Zadok Yohanna, da zai taka leda a bangaren maza.
