Matashin dan wasan Barcelona, Lamine Yamal, ya lashe kyautar gwarzon La Liga ta bana.
Ya gaji abokin wasansa Raphinha, wanda ya lashe kyautar a shekarar 2025.
Duk da fama da raunuka, Yamal ya taka rawar gani a kakar wasan.
Ya zura kwallaye 16 tare da bayar da taimako 12 a wasanni 28.
Rawar da ya taka ta taimaka wa Barcelona lashe kofin La Liga.
