Gwamnatin Tarayya ta fara shirin dawo da ‘yan kasarta sama da 1,000 daga Afirka ta Kudu yayin da ake kara nuna damuwa kan karuwar kyamar baki a Afirka ta Kudu.
Ma’aikatar harkokin wajen Najeriya ta tabbatar a ranar Juma’a cewa tantancewa don shirin dawo da wadanda suka amince ta fara ne a ranar Alhamis, inda hukumomi ke sa ran ‘yan Najeriya sama da 1,000 za su dawo.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin waje, Kimiebi Ebienfa, ya shaida wa AFP cewa har yanzu ba a tantance adadin karshe na masu son komawa gida ba, amma ya lura cewa ana sa ran adadin zai haura 1,000.
-
Gwamnati ta yi alkawarin ci gaba da murkushe ‘Yan Ta’adda
-
2027: A barwa Mata Kujerar Mataimakan Gwamna a Jihohi 36
“Ba a fitar da jimillar adadi ba tukuna, muna sa ran sama da mutum 1,000,” In ji Ebienfa.
Wannan mataki ya biyo bayan irin matakin da kasar Ghana ta dauka, wacce a kwanan nan ta dawo da daruruwan ‘yan kasarta daga Afirka ta Kudu saboda karuwar fargaba kan zanga-zanga da tashin hankali da baki haure ke ciki a kasar.