Gwamnatin Tarayya ta bukaci ‘yan Najeriya, kafafen yada labarai, kungiyoyin farar hula da hukumomin tsaro su hada kai wajen yaki da ta’addanci da ke barazana ga zaman lafiya da tsaron kasa.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da ya kira a Abuja.
Ministan ya ce yaki da ta’addanci na bukatar hadin kai ba tare da la’akari da bambance-bambancen siyasa, addini ko kabila ba.
Mohammed Idris ya nanata cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta kuduri aniyar ganin an kubutar da dalibai da malamai da aka sace a jihohin Oyo da Borno, tare da kara kaimi wajen tattara bayanan sirri da gudanar da ayyukan ceto.
Idris ya ce hukumomin tsaro sun samu nasarori a sassa daban-daban na kasar nan wajen yakar ‘yan ta’adda da masu aikata laifuka.
Ya bukaci ‘yan Najeriya su kasance masu sanya ido tare da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai domin tabbatar da tsaro a fadin kasar.
