Burin samar da ‘yan sandan jiha a Najeriya na kara kusantowa, biyo bayan ci gaba da aka samu wajen samar da dokar rarraba ikon aikin ‘yan sanda a kundin mulkin kasa, kamar yadda Fadar Shugaban Kasa ta bayyana.

Wannan ci gaban ya biyo bayan shafe watanni ana tattaunawa tsakanin Fadar Shugaban Kasa, Majalisar Dokoki da kuma hukumomin tsaro da nufin karfafa tsarin tsaron kasar.

Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila, ya bayyana haka a ranar Alhamis, lokacin da yake yi wa Manema Labarai karin bayani, a karshen taron tuntuba da Fadar Shugaban Kasa ta kira a Abuja.

Gbajabiamila ya bayyana cewa abin da aka sa a gaba yanzu shi ne tabbatar da gyaran kundin tsarin mulki, sai kuma dokokin da za su ba da damar hakan.

Kazalika, Ofishin mai baiwa Shugaban Kasa Shawara kan yada Labarai Bayo Onanuga, ya fitar da wata sanarwa kan tsarin samar da ‘yan sandan jiha, da aka fara gabatarwa game da batun na ‘Yan Sandan jihohi.

“Mun fara tattaunawa a cikin watanni uku ko hudu da suka wuce kan yadda za a bi wajen kafa ‘yan sandan jiha kamar yadda Shugaban Kasa ya umarta,” a cewar Onanuga.

Sai dai wasu na sukar batun da cewa a karshe za’a karawa Gwamnoni karfi ne domin farautar abokan hamayya, da kuma yiuwar  karancin kudaden gudanarwa, da yiwuwar ruruta rikicin kabilanci.

Sai dai kuma yunkurin kafa ‘yan sandan jiha ya zo ne a dai-dai lokacin da matsalar tsaro da sace-sacen mutane ke kara tsananta a sassan kasarnan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *