Masu Zanga-Zangar basu samu samu sukunin hallara a Dandalin Eagle Square dake Abuja ba

Masu Zanga Zangar, da suka yiwa take da “Free Our Children” ta haifar da tsaiko a wasu manyan titunan Birnin Tarayya Abuja a ranar Alhamis.

Masu Zangar-Zangar dauke da kwalaye da aka rubuta “Tinubu Must Go” sun tsaya Cak akan Titin Shehu Shagari Way, Daura da Babbar kotun Tarayya, sakamakon shingaye na tsaro da aka gindaya.

Fitaccen dan Gwagwarmaya Omoyele Sowore da wasu kungiyoyin fararen Hula ne suka shirya zanga-zangar a ranar Alhamis, domin nuna bacin rai kan abinda suka kira da tabarbarewar tsaro.

Rahotanni sun tabbatar da cewa masu Zanga-zangar sun shirya yin sansani a filin Eagle Square, inda daga nan ne zasu yi tattaki zuwa Fadar Shugaban kasa kamar domin gabatar da koken su.

Tun da farko sun hallara a lambun Millenium Park, wanda daga nan ne suka yi tattaki akan Babban Titin Shehu Shagari, inda suka karasa Babbar Mahadar da zata koma ofishin jamian tsaro na farin kaya, domin karasawa Dandalin Eagle Square.

Rashin samun damar zarcewa sakamakon shingayen tsaro ya sanya su juyowa suna rera wakoki dake alakanta shugaban kasar da masu garkuwa, tare da kiran sunayen wasu manyan kasar da suka hadar da Babban Sakataren gwamnati da kungiyar Boko Haram.

Zanga-Zangar ta Karkare ne da tsakar rana, bayan da Omoyele Sowore ya gabatar da jawaban gargadi kamar yadda ya saba ga gwamnatin Tarayya game da gaggauta kwato daliban da aka sace a jihar Oyo.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *