CP Ahmed ya bukaci mazauna Babban Birnin Tarayya Abuja su kai rahoton duk abinda suke da shakku akai

Kwamsshinan ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya Abuja CP Ahmed Muhammad Sanusi ya karyata rahoton cewa an yi garkuwa da mutane a Makarantar Firaimare ta Gbagalape dake Nyanya.

Wata Sanarwa da Kwamishina CP Ahmed Muhamamd Sanusi ya aikowa Blueprint Radio a ranar Alhamis, yace ofishin rundunar dake shiyyar Nyanya, ya karɓi kiran gaggawa cewar ana tsaka da garkuwa da mutane a makarantar firaimaren.

Sakamakon haka Rundunar ta bazama zuwa inda akace abin yana faruwa tare da kulle duk wata mashiga da mafita.

“Sai dai binciken farko da rundunar ta gudanar ya nuna cewa, ɗaliban makarantar ne kawai suka fara ihu suna fa ɗin “masu garkuwa”, daga bisani kuma suka riƙa tserewa daga cikin makarantar”. – A cewar Sanarwar.

Kwamishinan yace binciken da rundunar ta gudanar ta gano cewa babu abinda ya faru, domin babu wanda aka sace ko aka ce ba’a gani ba, haka kuma babu wadanda ake zargi ko kuma shaidun gani da ido.

CP Ahmed ya bukaci al’umma su kwantar da hankalinsu, sannan su guji yaɗa labarai marasa tushe, waɗanda ka iya haifar da fargaba a cikin al’umma.

Sannan ya buƙaci mazauna babban birnin tarayya da su gaggauta kai rahoton duk wani motsi na zargi ko abubuwan da basu gamsu da su ba ga ofishin ’yan sanda mafi kusa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *