Rundunar ‘yan sandan Jihar Filato ta ce ta kama mutane hudu da ake zargi suna da hannu wajen kashe wani matashi mai suna Ibrahim Mbaya, mazaunin yankin Rayfield da ke Karamar Hukumar Jos ta Kudu.
A wata sanarwa da ya fitar, Jami’in Hulda da Jama’a na rundunar, Alfred Alabo, ya ce wadanda ake zargi da aikata laifin kisan sun zargi mamacin da sace waya kirar iphone 12.
“Maimakon su kai kara zuwa ga hukumomin tsaro sai suka zabi daukar doka a hannunsu, suka kai wa mamacin farmaki, inda suka yi masa duka har ya fita a hayyacinsa,” Inji sanarwar.
- Tinubu zai sake ƙarawa sojoji albashi- Christopher Musa
-
Kotu ta yanke wa shugaban masu safarar ƙwayoyi da tsohon ɗan wasan ƙwallo hukuncin shekaru 24
-
Soji sun ceto mutane 48 da aka yi garkuwa da su a Zamfara
Rundunar ‘yan sandan ta kuma ce ta mika wadanda ake zargin zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuffuka (SCID) dake Helkwatarta a Jos, domin fadada bincike.
Har ila yau, Rundunar ta shawarci al’umma su guji daukar doka a hannu, da a karshe ke zamantowa nadama.