Ministan tsaro na Najeriya, Janar Christopher Musa (mai ritaya)

Ministan tsaro na Najeriya, Janar Christopher Musa (mai rita), ya bayyana cewa kwanan nan Shugaba Ahmed Bola Tinubu zai sanar da ƙarin albashi ga sojojin kasar.

Janar Musa ya bayyana hakan ne ranar Litinin, a Abuja, yayin taron kwana daya na horarwa da kuma bayar da tallafin kuɗi ga matan sojojin da suka rasu da kuma waɗanda ke raye , kuma ke ci gaba da aiki.

A cewar Janar Musa, “Ina son na sanar da ku cewa a makon da ya gabata, na ce sojoji yanzu suna karɓar naira 100,000, Lokacin da nake riƙe da muƙamin Babban Hafsan Sojin Ƙasa, ana biyan sojoji naira 49,000.

“Kusan shekaru biyu da suka wuce, na nemi a ƙara musu zuwa 100,000 kuma aka cimma hakan.  Sai dai, har yanzu, muna neman a sake ƙara musu-

“Ina da ƙwarin gwiwar cewa kwanan nan, Shugaban Ƙasa zai sake sanar da ƙarin albashi ga dakarun mu,” In ji shi.

Al’ummar Najeriya na ci gaba da tafka muhawara a kafafen sadarwa game da albashin naira 100,000 da gwamnati ta ce tana biyan ƙananan sojoji, duba da yadda kayan masarufi ke ƙara tsada a kasuwanni da kuma sadaukarwar da suke yi ga ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *