Wani da ke kiran kansa Darakta-Janar, Yarima Adeniyi Adeyemi Matthew, ana zargin ya gudanar da wannan hukuma ta gwamnatin tarayya daga Sakatariyar Tarayya da ke Abuja na tsawon shekara guda, inda har ya sami kasafi na naira biliyan 1.3 a cikin kasafin kudin tarayya na shekarar 2026 kafin a fallasa shi kuma aka kama shi a kan zargin jabu da sojan gona.
Ana zargin Yarima Adeniyi Adeyemi ya yi amfani da takardun jabu, har ma da jabun sa hannun Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila, domin ya nuna kansa a matsayin halatacciyar hukumar gwamnati, inda ya gana da jakadun kasashen waje, ya tura ma’aikata aiki, kuma ya sami babban ofis.
An yi nasarar shigar da hukumar ta bogi a cikin kasafin kuɗin ƙasa a ƙarƙashin lamba 0111062001, ɗauke da kiyasin kuɗi naira biliyan 1.3 don manyan ayyuka da kuma kuɗaɗen gudanarwa.
Babban Bankin Najeriya (CBN) ya tabbatar da cewa an buɗe asusun banki na ƙetare (domiciliary accounts) domin wannan bogizumar kungiya, ko da yake bincike ya nuna cewa asusun ba su yi wani aiki ba kuma babu ko sisi a ciki.
- Fubara bai yi wani laifi ba — Wike
- Kotun ɗaukakaƙara ta soke hukuncin da ya umarci a soke rajistar ADC, Accord da sauran Jam’iyyu
- Na gamsu da yadda aka zamanantar da NTA — Minista
Gwamnatin tarayya ta bayyana Adeyemi a matsayin tsantsar dan damfara kuma mai sojan gona wanda yake da tarihin aikata manyan laifuka. Fadar Shugaban ƙasa ta jaddada cewa hukumar ba kafa ta ta fuskar doka ba, kuma an yi amfani da takardun jabu ne aka gudanar da harkokin ba tare da wani izini na hukuma ba.
Hakazalika, ƙungiyoyin fafutuka da ‘yan majalisa suna jayayyar cewa aiki mai girman wannan; wanda ya haɗa da samun ofis a Sakatariyar Tarayya, tantance kasafin kuɗi, da samun damar shiga harkokin banki—yana nuna gazawar tsarin gwamnati da kuma yiwuwar samun hadin baki daga manyan jami’an cikin gwamnati.
Wannan ta sa hukumar Yaki da Fasadi da Sauran Laifuka Masu Alaka (ICPC) da kuma wani kwamiti na musamman a Majalisar Wakilai sun ƙaddamar da bincike domin gano yadda tsarin tantancewa, sa ido na ma’aikata, da tsarin kasafin kuɗi na majalisa suka gaza gano wannan kungiya da wuri.
Game da Adeniyi Adeyemi kuwa, bayan da ya kwashe lokaci yana cewa rayuwarsa na fuskantar barazana, jami’an tsaro na Intelligence Response Team (IRT) sun yi nasarar kama shi a maɓoyarsa da ke Jihar Osun, biyo bayan sammacin da Babbar Kotun Tarayya ta fitar.
Har ila yau, a zaman da aka yi ranar Litinin, Kwamitin Musamman na Majalisar Wakilai ya ba Sufeto-Janar na Yan Sanda (IGP) umarni mai tsanani na lallai ya gabatar da Adeyemi a gaban majalisa don fuskantar tambayoyi game da ayyukan hukumar bogi ta PFIPC.
Hukumar Yaki da Fasadi ta ICPC ta riga ta gayyaci Femi Gbajabiamila kuma ya bayyana a hedkwatarsu inda aka yi masa tambayoyi dangane da zargin da Adeyemi ya yi masa na cewa an ba shi cin hancin ₦400 miliyan.
A gefe guda kuma, majalisar Wakilai tana fuskantar gagarumin matsin lamba daga kungiyoyin fafutuka da ‘yan adawa don su ma su aiko masa da sammacin bayyana a gabansu.
Sai dai har yanzu shi Gbajabiamila ya musanta sanin hukumar, yana mai cewa an yi jabun sa hannunsa ne, kuma tuni ya shigar da ƙarar neman diyyar naira biliyan15 a kotu.
Cikin masu matsawa majalisar lambar sai ta gayyato Gbajabiamila, akwai Babban lauyan Femi Falana mai fafutuka.
Ya fito fili ya bayyana cewa fadar shugaban ƙasa ba ta da ikon wanke kowa a wannan badaƙala.
Falana ya buƙaci lallai a gudanar da bincike mai zaman kansa wanda zai haɗa da titsiye Gbajabiamila.
Ita ma ƙungiyar Resource Centre for Human Rights and Civic Education (CHRICED) ta fitar da sanarwa ta hannun babban daraktanta, Ibrahim M. Zikirullahi, inda ta buƙaci a dakatar da Gbajabiamila daga ofis sannan majalisa da sauran hukumomi su titsiye shi.
Bugu da ƙari, kungiyoyi irin su HURIWA (Human Rights Writers Association of Nigeria), ƙungiyar Afenifere, da dai sauransu duk suna cikin sahun gaba wajen matsa lamba.
Haka zalika, su ma Jam’iyyun Adawa kamar su NDC da ADC na cikin masu matsa lambar don tabbatar da cewa ba a rufe maganar ba, inda suke fargabar cewa idan ba a tursasa shi ya bayyana a majalisa ba, jami’an gwamnati na iya kare juna.
Dalilan masu fafutuka da matsa lambar sai an gayyato Gbajabiamila na ganin cewa tun da hukumar yaƙi da cin hanci ta ICPC ta riga ta gayyato Gbajabiamila kuma ya amsa tambayoyi kan zargin karɓar naira miliyan 400, bai dace Majalisar Wakilai ta nuna jinkiri ko tsoron aika masa da tata gayyatar ba domin tona asirin yadda aka shigar da hukumar bogi a kasafin kuɗin ƙasa.
Abin jira a gani dai shi ne ko Majlisar Wakilan Najeriyar za ta iya gayyato wanda ya taba zama Shugabanta a wani lokaci don amsa irin wannan tuhume-tuhume akan sa, musamman ma idan aka yi la’akari da irin dangantakarsa da Shugaban Majalisar na yanzu da akasarin ‘ya’yan Majalisar?
Lokaci ne kadai zai iya fayya ce hakan.