Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke zamanta a Abuja ta soke hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ya umarci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta soke rajistar jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Accord Party da wasu jam’iyyun siyasa uku.

Kotun ta bayyana cewa hukuncin da ya umarci INEC ta soke rajistar waɗannan jam’iyyu “ba shi da inganci kuma babu tasirinsa a doka.”

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, a baya Mai Shari’a Peter Lifu na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ya umarci INEC ta soke rajistar jam’iyyun bisa yadda suka taka rawa a babban zaɓen 2023.

Sai dai jam’iyyun siyasar da abin ya shafa, ciki har da ADC da Action Peoples Party (APP) da Action Alliance (AA) da Accord Party (AP) da Zenith Labour Party (ZLP), sun ɗaukaka ƙara suna neman a soke wannan hukunci.

Kotun Ɗaukaka Ƙarar ta bayyana hukuncin Babbar Kotun Tarayyar a matsayin “marar inganci”, tana mai cewa abin da kotun ta yi ya kasance keta iyakar ikon shari’a, ko kuma abin da Kotun Koli ta bayyana a matsayin rashin biyayya ga tsarin ikon kotuna (judicial insubordination).

Kwamitin alkalan kotun guda uku, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Abba Mohammed, ya yanke hukuncin baki ɗaya cewa Babbar Kotun Tarayya ba ta da hurumin sauraron shari’ar tun daga farko.

Kotun ta kuma ce Babbar Kotun Tarayya ta yi kuskure da ta ci gaba da yanke hukunci duk da cewa Kotun Ɗaukaka Ƙara ta riga ta bayar da umarnin dakatar da ci gaba da shari’ar, ciki har da dakatar da yanke hukunci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *