Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Osun ta sanar da fara bincike kan harin da ake zargin ‘yan daba ne suka kai wa jami’an Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) a Ƙaramar Hukumar Odo-Otin, inda suka yi awon gaba da wasu katunan zaɓe na dindindin (PVCs).
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, DSP Abiodun Ojelabi, ya fitar a ranar Lahadi a birnin Osogbo.
- NDLEA ta kama miyagun kwayoyi na sama da naira biliyan 10, ta cafke manyan masu safarar su
- INEC ta sanar da rufe aikin rijistar katin zaɓe a yau Lahadi
- Soji sun ceto mutane 48 da aka yi garkuwa da su a Zamfara
A cewar sanarwar, jami’an INEC na gudanar da rabon katunan zaɓe na dindindin (PVCs) a Makarantar Firamare ta Oyinlola DC, Ward 2, da ke Ƙaramar Hukumar Odo-Otin, lokacin da wasu kimanin mutum goma dauke da makamai suka kai musu hari.
An ce maharan sun riƙa harbe-harbe a sama domin tsoratar da jama’a kafin su gudu da fakiti uku na katunan PVC.
Kakakin rundunar ya ce Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Osun, Ibrahim Gotan, ya yi Allah wadai da harin, tare da umartar a gudanar da cikakken bincike domin gano waɗanda suka aikata laifin, kama su da kuma gurfanar da su a gaban kotu.
Ojelabi ya ƙara da cewa rundunar ta tura jami’an musamman da na tattara bayanan sirri domin farautar waɗanda ake zargi, tare da ƙara ƙaimi wajen ƙwato katunan PVC da aka sace.