Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta sake jaddada cewa za ta kammala aikin rijistar masu zaɓe na CVR, a yau Lahadi, 26 ga watan Yuli.
Da wannan ne, INEC, ta buƙaci ‘yan Najeriya da suka cika sharadi da su yi amfani da damar ƙarshe domin yin rijista ko sabunta bayanan katin zaɓen su.
Hukumar ta sanar da hakan ne cikin sakon da ta wallafa a shafinta na X a yau Lahadi, inda ta jaddada cewa yin rijistan na da matukar muhimmanci ga duk wanda ke son kaɗa kuri’a a zaɓen 2027 na ƙasa baki ɗaya.
-
Akwai bukatar ƙasashen Afirka su yi amfani da albarkatun ƙasarsu don samun matsayi a kasuwannin duniya – Shettima
-
Soji sun ceto mutane 48 da aka yi garkuwa da su a Zamfara
-
Sojoji sun fara aikin ceto Shugaban ƙaramar Hukumar Bunguɗu
“Lokaci na gudu, amma har yanzu kana da damar da za ka sa a ji muryar ka,” in ji hukumar INEC.
“Ka yi rijista don kaɗa kuri’a ko sabunta bayanan ka na zaɓe kafin a rufe rijistar masu zaɓe na CVR a yau, Lahadi, 26 ga Yuli 2026.”

INEC ta ce ‘yan Najeriya da ba su yi rijista ba tukuna za su iya kammalawa ta hanyar shiga shafin CVR na hukumar a yanar gizo, ko su je ofisoshin hukumar na Jiha da Ƙananan Hukumomi kafin a rufe gudanar da aikin.
INEC ta ƙara da cewa aikin rijistar ya haɗa da neman canja wurin zaɓe, gyara bayanan mutum, neman sabon katin zaɓe na dindindin (PVC) idan na baya ya ɓata ko ya lalace.
INEC ta shawarci duk masu son yin rijista kada su ƙara jinkiri, inda ta jaddada cewa yin rijistar zaɓe yana da matuƙar muhimmanci ga duk ɗan ƙasa da ke son shiga zaɓen da za a yi a shekara ta 2027.