Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya ce Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara bai aikata wani laifi ba bayan sulhun da ya yi da ɓangaren siyasar Wike, yana mai cewa “a siyasa babu abin da ake kira zunubi.”
Wike ya ce matakin da Fubara ya ɗauka na komawa cikin gidan siyasar da ya fito daga cikinsa shi ne mataki mafi dacewa, kuma hakan zai ƙarfafa yunƙurin tattara goyon baya domin sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a shekarar 2027.
Ministan ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin da yake zantawa da manema labarai bayan duba ayyukan gina hanyoyi da ake ci gaba da yi a Babban Birnin Tarayya.
- Kotun ɗaukakaƙara ta soke hukuncin da ya umarci a soke rajistar ADC, Accord da sauran Jam’iyyu
- Na gamsu da yadda aka zamanantar da NTA — Minista
- Majalisar Wakilai ta umarci Sufeto Janar na ’yan sanda ya gabatar da daraktan hukumar bogi Adeyemi Cikin Sa’o’i 48
Kalaman nasa sun biyo bayan sanarwar da Fubara ya yi kwanaki kaɗan da suka gabata, inda ya bayyana goyon bayansa ga Rainbow Coalition na Wike, ya amince da sake tsayar da Shugaba Tinubu takara a wa’adi na biyu, sannan ya buƙaci magoya bayansa su mara wa ƙawancen baya.
Wike ya tunatar da cewa tun a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a baya ya bayyana cewa Fubara ba shi da wani zaɓi face ya koma gidan siyasar da ya fito.
Ministan ya ƙara da cewa komawar Fubara cikin tafiyar siyasar Wike za ta taimaka wajen samun ƙuri’un da ake buƙata domin sake zaɓen Shugaba Tinubu.