Rundunar ‘Yan sanda ta dakile wani yunkurin garkuwa da mutane a Byazhin dake yankin kubuwa a Abuja, sun kwato bindigar AK-47
Jami’an sashen yaki da garkuwa da mutane sun isa yankin ne,bayan samun bayanan sirri da misalin karfe 12 da Rabi na dare, a dai dai lokacin da maharan ke kokarin shiga wani gida domin yin garkuwa da mazaunan sa.
Musayar wuta mai tsanani ta biyo baya wadda ta dauki sama da mintuna 30 inda maharan suka tsere zuwa cikin daji dauke da raunukan harbin bindiga inda aka kwato bindiga kirar AK-47 da kwankson alburusai da kuma Alburusan bakwai.
- Abuja: ‘Yan bindiga sun hallaka ‘Dan Banga
-
Dakarun OPHK sun ceto waɗanda aka yi garkuwa da su a Maiduguri
An ceto Mista Samson da matarsa ba tare da sun samu rauni ba yayin da Kwamishinan ‘Yan Sandan FCT ke yabawa jami’an tare da tabbatar da ci gaba da tsaro a Abuja.
