NCDC ta ƙara matakan rigakafin Ebola yayin da haɗarin shigowarta Najeriya ke ƙaruwa.
Hukumar Cututtuka ta Najeriya ta ce haɗarin shigowar Ebola ya ƙaru ne saboda yaduwa a Gabashin Afirka da zirga-zirgar mutane.
Darakta-Janar na Hukumar, Dakta Jide Idris, ya ce duk da babu Ebola a Najeriya, ana ƙara matakan kariya da sa ido a iyakoki da dakunan gwaje-gwaje.
- Karancin ruwa yayi ajalin mutane 49 a Hamada dake Jamhuriyar Nijar
- Ambaliya: Ghana na asarar Dala Miliyan 200 duk shekara -GMet
Ya kuma ja hankalin Jihohi da ma’aikatan lafiya su ƙara shiri da horo don gano cutar cikin gaggawa tare da haɗin gwiwa don kare Najeriya.
