Mutanaen da suka rasu a saharar Nijar

Kimanin mutane 49 sun rasu a cikin hamadar Sahara dake iyakar Nijar da Mali da Aljeriya dake da tazarar km 80 a yammacin Asamaka

Wata sanarwa daga ofishin Gwamnan jihar Agadez Janar Ibra Boulama, tace matafiyan nacikin wata  babbar motar da ke dauke da mutanen da aka kiyasta cewa sun haura 40

A cewar wasu shaidu motar ta taso ne daga kauyen Telhandek da ke da tazarar km 300 da iyakar Nijar dauke da wasu ‘yan kasar a kan hanyarsu ta zuwa gida domin shagulgulan sallar layya kafin direban ya yi batan Kai a hamada, lamarin da ya haddasa karancin ruwan sha da yayi ajalin mutanen

A kalla mutane 49 ne aka yi jana’izar su a wurin da abin ya faru a cewar ofishin Gwamnan Agadez yayin da wasu mutane 2 daga cikin fasinjojj suka tsira da ransu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *