Babban Hafsan Sojin Ruwan Najeriya Idi Abbas, ya ce abune mai wahala a iya kama mutanen da ke shirya makarkashiyar satar danyen mai a kasarnan.
Idi Abbas ya bayyana hakan ne a shirin “Sunrise Daily” na gidan Talabijin din Channels, a ranar Jumma’a, inda yace mafi yawancin wadanda ake kamawa basu da cikakkiyar masaniyar yadda al’amarin yake.
Riya Admiral Abbas ya ce mutanen da ke shirya satar Man suna amfani ne da wani tsari mai sarkakiya, dake baiwa bangaren shari’a wahala wajen gurfanarwa da kuma bin diddigin bayanan sirri.
“Wadanda muke kamawar a mafi yawan wuraren tace mai na bogi ana ba su kudi kalilan ne, yayin da manyan ‘yan damfarar ke cin riba mai yawa, kuma ba zaka taba sanin su waye ba.” in ji shi.
-
Najeriya za ta dawo da ‘yan kasarta daga Afirka ta Kudu
-
Yamal ya lashe kyautar gwarzon dan wasan La Liga
“A kokarin gurfanar da wasu daga cikin mutanen da muke kamawa, wasu daga cikinsu ba su ma san wanda suke yi wa aiki ba. Don haka, akwai sarkakiya a hanyoyin sadarwar su,” a cewar Abbas.
Duk da kalubalen, Shugaban Sojojin ruwan ya ce Rundunar Sojin Ruwan Najeriya da sauran hukumomin tsaro na ci gaba da inganta dabarun dakile sabbin hanyoyin da masu satar mai ke amfani da su.
Satar danyen mai, musamman a yankin Neja Delta, na ci gaba da yi wa Najeriya asarar biliyoyin kudaden shiga a kullum, tare da haddasa lalacewar muhalli ga al’ummomin da abin ya shafa.

[…] Zai yi wuya ka gano wadanda ke shirya satar Danyen Mai – Admiral Idi Abbas […]