Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kai hari, wani yanki na Babban Birnin Tarayya, Abuja, ranar Asabar, inda suka sace wani mazaunin yankin.

Maharan sun kuma hallaka mutum guda lokacin da suka shiga Unguwar Quarry dake yankin Kubwa, da misalin karfe 11 na dare, a cewar Jaridar PUNCH.

Da yake zantawa ta wayar tarho da Jaridar Punch a ranar Litinin, sakataren al’ummar yankin mai suna Dairo, ya ce, “Mun jiyo karar harbe-harbe, a harabar wani gida dake kusa da tsauni. Amma jami’an tsaron unguwa sun yi kokarin dakile harin.”

Dairo ya bayyana cewa duk da namijin kokari daga jami’an tsaron unguwan, maharan sun samu nasarar shiga gidan wanda abin ya shafa.

“Sun iya shiga dakin mutumin. Sun harbe shi sannan suka tafi da kanensa,” in ji sakataren.

Ya kara da cewa jami’an ‘yan sanda sun iso jim kadan bayan harin, amma masu garkuwar sun riga sun tsere da wanda suka sace.

Sakataren al’ummar ya bayyana lamarin a matsayin garkuwa da mutane na uku da mahara suka yi nasara a yankin a ‘yan shekarun nan.

Kokarin jin ta bakin mai magana da yawun ‘Yan Sandan Abuja, Josephine Adeh, ya ci  tura, haka kuma lambobin wayarta ba sa shiga.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *