Faɗuwar Jirgin na zuwa ne yayin da ake tsaka da musayar wuta tsakanin Iran da Isra’ila, lamarin da ke barazana ga tattaunawar ƙarfafa yarjejeniyar tsagaita wuta.
Jim kadan da faduwar jirgin Shugaban Amurka Donald Trump, ya bayyana cewa Matuƙan jirgin suna nan lafiya.
Trump ya yi wannan kalamai ne a ranar Litinin, a filin Jirgi na ƙasa da ƙasa na John F. Kennedy, bayan kammala kallon wasan ƙarshe na gasar wasan ƙwallon kwando na NBA a birnin New York,
Jaridar The New York Times ce ta fara ba da rahoton cewa wani jirgi sojin Amurka mai saukar angulu ya faɗi a kusa da mashigar ruwan, a cikin wani yanayin da ba a tantance ba.
Babu cikakken bayani kan ko makaman Iran ne suka harbo jirgin ko ya samu matsalar na’ura ne ko kuma wata matsala ta daban ce ta janyo faɗuwar, in ji rahoton.
Fadar White House da Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka da kuma Cibiyar Tsaron Amurka ba su mayar da martani nan take ba ga buƙatar neman tsokaci da aka tura musu.