Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta sanar da cewa Florentino Pérez ya sake lashe zaben shugabancin kungiyar, inda zai ci gaba da jagorantar kungiyar ta kasar Spaniya.
A wata sanarwa da hukumar kungiyar ta fitar a shafin ta ranar Litinin, Hukumar Zabe ta kungiyar ta ce, “Bayan an kammala kirga dukkan kuri’un da aka kada ‘yan takarar da Mista Florentino Pérez ke jagoranta sun lashe zaben Shugaba da Kwamitin Daraktoci na Real Madrid.”
“‘Yan takarar da Mista Florentino Pérez ke jagoranta sun samu kuri’u 21,741, wanda ke wakiltar kaso mafi rinjaye na 65 cikin dari,” -in ji sanarwar.
Abokin hamayyarsa, Enrique Riquelme, ya samu kuri’u 11,814, wanda ke daidai da kaso 35 na kuri’un.
“‘Yan takarar da Mista Enrique Riquelme ke jagoranta sun samu kuri’u 11,814, wanda ke wakiltar kaso 35%,” Hukumar Zaben ta kara da cewa.
Wannan nasara ta tabbatar da cewa Pérez zai ci gaba da zama shugaban Real Madrid, yana jagorantar Kwamitin Daraktoci wanda ya hada da Mataimakan Shugabanni Eduardo Fernández de Blas, Pedro López Jiménez, Enrique Sánchez González da Enrique Pérez Rodríguez.
Sake zabensa ya kara tsawaita jagorancin Pérez a Real Madrid, daya daga cikin kungiyoyin kwallon kafa mafi nasara a duniya, bayan ya samu rinjayen kuri’u daga mambobin kungiyar.
Pérez, ya yi alkawarin sayan manyan zakakuran ‘yan wasa, irin su Julian Alvarez, Erling Haaland da sauran su zuwa Madrid domin hana Barcelona yin katabus a kakar wasa mai zuwa.