Shugaban na INEC yace dole ne su garzaya gaban Kotun neman fassarar wasu sassa dake gogayya da juna game da zaben shekarar 2027

Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC), Farfesa Joash Amupitan, SAN, ya ce rashin daidaiton jadawali da tsare-tsaren gudanar da zaɓe zai haifar da ruɗani tare da kawo cikas ga ikon da kundin tsarin mulki ya bai wa hukumar na gudanar da zaɓe.

A cewarsa wannan ne dalilin da ya sa hukumar ta ɗaukaka ƙara kan wasu hukunce hukuncen Kotun Tarayya guda biyu da suka bukaci Karin haske kan wasu sassa na Jadawalin Zaɓen 2027.

Farfesa Amupitan ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 9 ga Yuni, 2026, yayin da yake gabatar da jawabin buɗe taron tuntuba  kashi na biyu na shekara-shekara tsakanin INEC da shugabannin jam’iyyun siyasa a hedikwatar ta da ke Abuja.

Ya shaida wa shugabannin jam’iyyun cewa a shari’a mai lamba FHC/ABJ/CS/517/2026 wadda aka yanke hukuncinta a ranar 20 ga Mayu, 2026, Kotun Tarayya ta nuna shakku kan wasu lokuta da aka tsara a jadawalin zaɓen hukumar.

Ya kuma ƙara da cewa a wata shari’a ta daban mai lamba FHC/ABJ/CS/720/2026 kotun ta sake yin tsokaci kan wasu batutuwan da suka shafi jadawalin zaɓen da hukumar ta fitar.

Amupitan ya ce saboda muhimmancin samun sahihin jadawali guda ɗaya da zai jagoranci dukkan masu ruwa da tsaki a harkar zaɓe, hukumar ta ga dacewar ɗaukaka ƙara domin neman ƙarin haske da tabbatar da matsayin doka kan lamarin.

Idan dai za’a iya tunawa INEC ta ware ranakun 16 ga watan janairun 2027 don gudanar da zaben shugaban kasa dana ‘yan Majalisar tarayya.

Yayin da za’a gudanar da zabukan Gwamnoni da na ’yan Majalissun Jiha a ranar 6 ga watan  fabarairu, lamarin daya jawo suka daga sassa daban daban na kasar nan cewar jadawalin farkon ya hade da lokutan Azumin Ramadana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *