Dan takarar gwamna na Jam’iyyar PDP a Jihar Gombe, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ya nuna farin cikinsa da labarin nasarar ceto dalibai 360 da aka sace a Borno.
A cikin wata sanarwa da ya wallafa ashafin sa ranar Talata, Pantami ya ce ceto daliban ya sanya matukar jin dadi ga iyalan da al’ummomin jihar Borno, da dukkan ‘yan Najeriya masu kishin kasa”.
Pantami ya ce Sojojin Najeriya da hukumomin leken asiri, masu sa kai na tsaron gida, da duk wanda ya shiga cikin wannan aikin sun yi abinda ya kamata, dake bukatar yaba musu.
-
Yaƙi da Ta’addanci na Al’umma ne ba Jami’an tsaro kaɗai ba – Tinubu
-
Yaɗa Bayanan Ƙarya na Barazana ga Tsaro – Janar Waidi Sha’aibu
Pantami ya kara da cewa, nasarar tunatarwa ce mai karfi cewa idan akayi azama da hadin kai, da kishin kasa, za’a iya shawo kan dukkanin wani kalubalen tsaro da ke fuskantar kasarnan komai girman sa.
Malamin yayi fatan al’ummar Najeriya zasu dage da addu’o’in tona asirin wadanda ke da hannu ko goyon bayan shigar kasar matsalolin ta’addanci, garkuwa da mutane da sauran muggan laifuka.
