EFCC na taka muhummiyar rawa wajen tabbatar da adalci da rikon amana

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar da sabon ginin ofishin Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati (EFCC) a Ado-Ekiti ranar Talata, 9 ga Yuni, 2026

Shugaban ya bayyana aikin a matsayin wani muhimmin shiri da zai taimaka wajen ƙarfafa sauye-sauyen yaƙi da cin hanci da rashawa da kuma aiwatar da manufofin “Sabunta Fata” na Gwamnatin Tarayya.

Shugaban wanda mataimakinsa Kashim Shettima ya wakilta, ya yaba wa Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, da daukacin jami’ai da ma’aikatan hukumar saboda jajircewarsu wajen ƙarfafa yaƙi da cin hanci da rashawa.

A cewar shugaban ƙasar, kammala wannan katafaren gini na zamani wata shaida ce ta ƙudurin EFCC na yin tasiri mai ɗorewa a rayuwar ’yan Nijeriya da kuma ƙarfafa yaƙi da cin hanci da rashawa a faɗin ƙasa.

Ya ƙara da cewa sabon ofishin zai taimaka wajen inganta ayyukan bincike, gurfanar da masu laifi gaban kotu, da kuma tabbatar da gaskiya da riƙon amana a harkokin Gwamnati da Jama’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *