Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya yaba wa jami’an tsaron Najeriya bisa Jarumta da sadaukarwar da suke nuna wa a yaƙi da ta’addanci, ƴan bindiga, masu garkuwa da mutane da sauran barazanar tsaro a faɗin ƙasar.

A wani saƙo da ya aike wa Rundunar ta shafinsa na X a ranar Litinin, shugaban ya yabawa dakarun da ke bakin daga.

Yana mai bayyana su a matsayin garkuwar da ke kare rayukan fararen hula tare da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a ƙasa.

Shugaban ya amince da cewa yanayin da jamian ke aiki bashi da dadi, na rashin kasancewar ‘yan uwansu na dogon lokaci da kuma damuwar da aikin tsaro ke haifarwa.

“Wannan yaƙi bai kasance mai sauƙi ba. Ya zo da raɗaɗi, matsin lamba da sadaukarwa. Amma jarumtarku ta kasance mai ƙarfi. Na yaba wa ayyukanku. Ina girmama sadaukarwarku. Ƙasarku ba ta ɗauke ku da wasa ba,” in ji Shugaban.

Godiyar Shugaban bata tsaya ga sojoji kaɗai ba, har ma ga jami’ai da ma’aikatan Rundunar ‘Yan Sanda, Hukumar Tsaron Farin Kaya ta DSS, Hukumar Tsaro da Kare Fararen Hula ta Najeriya (NSCDC), hukumomin leƙen asiri, ƙungiyoyin tsaron al’umma da sauran masu aiki wajen tabbatar da tsaron ƙasa.

Shugaban ya kuma karrama jami’an tsaro da suka rasa rayukansu yayin gudanar da aiki, yana mai cewa sadaukarwarsu ta zama ginshiƙi wajen tabbatar da rayuwar ƙasa da dorewar zaman lafiya.

Tinubu ya buƙaci ‘yan Najeriya da su tallafa wa hukumomin tsaro ta hanyar bayar da sahihan bayanai kan lokaci domin taimakawa wajen yaƙi da laifuka da ta’addanci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *